Volodymyr Zelensky
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da Hausa ana furta sunan shi da Zelenskai an haife shi a ranar 25 ga watan Janairu shekara ta 1978. Ɗan ƙasar Ukraniya ne, tsohon ɗan wasan kwaikwayo kuma ɗan wasan barkwanci wanda shi ne shugaban ƙasa na shida kuma shi ne shugaban ƙasar Ukraniya na yanzu.[1][2]
Zelenskyy ya girma a Kryvyi Rih, babban birni a yankin da ake magana da harshen Ukraniya a tsakiyar Ukraniya. ya sami digiri a fannin shari'a daga Jami'ar Tattalin Arziƙi ta Kyiv. Daga nan sai ya fara wasan kwaikwayo shi ne wanda ya ƙirƙiro kamfanin Kvartal 95, wanda ke samar da fina-finai, zane-zane/kaatuun, da kuma watsa fina-finai na shows TV cikin finafinan shi akwai Servant of the People, wanda Zelenskyy ya fito a matsayin shugaban kasar Ukraniya. Film ɗin mai dogon zango ya fito daga 2015 zuwa 2019 kuma ya shahara sosai ya samu ƙarɓuwa a gun jama'a. Ma'aikatan Kvartal 95 ne suka ƙirƙiro wata jam'iyyar siyasa mai suna iri ɗaya da sunan gidan talabijin ɗin shi (Shows TV) a watan Maris shekarar 2018.
Zelenskyy ya sanar da maganar tsayawa takararsa a zaɓen shugaban ƙasar Ukraniya na shekara ta 2019 a yammacin ranar 31 ga Disamba shekara ta 2018, tare da jawabin jajibirin sabuwar shekara na shugaban ƙasar Petro Poroshenko akan tashar talabijin ta 1+1 TV channel. Ɓangaren siyasa, ya riga ya zama ɗaya daga cikin masu fafutukar neman shugabanci a siyasance, ya lashe zaɓen ne da kashi 73.2 na ƙuri'un da aka kaɗa a zagaye na biyu, inda ya doke Poroshenk. An gane cewa shine ya shahara sosai a lokacin. ya yima kansa laƙabi da ɗan gwagwarmayar kafa sabbin cigaba (anti-establishment), da kuma wargaje cin hanci da rashawa (anti-corruption).
A matsayinsa na shugaban ƙasa, Zelenskyy ya kasance mai goyon bayan gwamnatin zamani ta e-government da haɗin kai tsakanin sassan ƙasar Ukraniya da masu magana da harshen Rashanci. Salon yadda yake amfani da kafofin watsa labarun yana burgewa sosai, musamman a Instagram .
Gwamnatin Zelenskyy ta fuskanci babban hatsaniya da ƙasar Rasha a cikin shekara ta 2021, wanda a ƙarshe taƙaddamar ta haifar da har sai da shugaban ƙasar Vladimir Putin Rasha ya bada umurnin sojojin Rasha su mamaye ƙasar Ukraniya a watan Fabrairu shekara ta 2022. Dabarar Zelenskyy a lokacin da Rasha ta girke sojojin ta don mamaye Ukraniya ita ce kwantar da hankalin al'ummar Ukraniyawa tare da tabbatar wa ƙasashen duniya cewa Ukraniya ba ta neman daukar fansa akan Rasha. Bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraniya, Zelenskyy ya ayyana dokar-ta-ɓaci a duk faɗin ƙasar da taron gama gari.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Dickinson, Peter (9 June 2019). "Zelensky, Zelenskiy, Zelenskyy: Spelling Confusion Doesn't Help Ukraine". Atlantic Council (in Turanci). Archived from the original on 11 June 2019. Retrieved 10 June 2019.
- ↑ Mendel, Iuliia [@IuliiaMendel]. "Dear colleagues, this is the official form of the last name that the President has in his passport. This was decided by the passport service of Ukraine. The President won't be offended if BBC standards assume different transliteration" (Tweet) (in Turanci). Archived from the original on 12 November 2020. Retrieved 10 June 2019 – via Twitter.