Auvers-sur-Oise
Auvers-sur-Oise | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Oise (en) | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Faransa | ||||
Administrative territorial entity of France (en) | Metropolitan France (en) | ||||
Region of France (en) | Île-de-France (en) | ||||
Department of France (en) | Val-d'Oise (en) | ||||
Babban birnin | |||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 6,763 (2021) | ||||
• Yawan mutane | 532.94 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Located in statistical territorial entity (en) |
Q108921672 Paris unité urbaine (en) | ||||
Yawan fili | 12.69 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Oise (en) | ||||
Altitude (en) | 28 m-21 m-111 m | ||||
Sun raba iyaka da |
Nesles-la-Vallée (en) Butry-sur-Oise (en) Ennery (en) Hérouville-en-Vexin (en) Mériel (en) Méry-sur-Oise (en) Pontoise (en) Saint-Ouen-l'Aumône (en) Valmondois (en) | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Ta biyo baya | Butry-sur-Oise (en) | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
• Mayor of Auvers-sur-Oise (en) | Isabelle Mezières (en) (28 ga Maris, 2014) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 95430 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | ville-auverssuroise.fr |
Auvers-sur-Oise ( furuci da Faransanci: [Ovɛʁ syʁ waz], yana nufin Auvers on Oise ) gari ne a yankin Val-d'Oise, a arewa maso yammacin Paris, Faransa. Garin na da nisan kilomita 27.2 kilometres (16.9 mi) daga tsakiyar Paris. Akwai shahararrun masu zane a garin da dama, mafi mashahuri shine Vincent van Gogh . Wannan shine wurin da van Gogh ya mutu, ga dukkan alamu ta hanyar kashe kansa.
Yanayin kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Wuri
[gyara sashe | gyara masomin]Auvers na nan a bangaren daman kogin Oise . Daga kudu kuwa tana haɗe da Méry-sur-Oise ta hanyar wata gada.Samfuri:Adjacent communities
Yankuna
[gyara sashe | gyara masomin]- Chaponval
- Cordeville (daga Corbeville)
- Le Montcel (daga Monsellus, ƙaramin dutse)
- Les Vaissenots ko Vessenots
- Le Valhermeil (daga Val Hermer, sunan mai shi a cikin karni na 12)
- Les Vallées
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin karni na 19, masu zan da dama sunyi rayuwa a garin kuma sun yi aiki a Auvers-sur-Oise, ciki har da Paul Cézanne, Charles-François Daubigny, Camille Pissarro, Jean-Baptiste-Camille Corot, Norbert Goeneutte, da Vincent van Gogh . Gidan Daubigny a yanzu ya zama gidan kayan gargajiya inda mutum zai iya ganin zane-zanen Van Vough, danginsa, da abokansa, irin su Honoré Daumier, da kuma ɗakunan da aka yi wa ado a cikin salo na wancan zamanin. Charles Sprague Pearce (1851-1914) shima anan ya mutu. A gefen kogin daga Auvers zuwa Pontoise akwai wurare da yawa waɗanda ke cikin zanen Pissarro.
A lokacin karni na 20 masu zane sun ci gaba da ziyartar Auvers, ciki har da Henri Rousseau ( Douanier Rousseau ), Otto Freundlich da Pierre Daboval . Mai zane COBRA mai suna Corneille ya shafe shekarunsa na ƙarshe a ƙauyen kuma an binne shi a 'yan mitoci kaɗan daga Vincent van Gogh.[1]
Yawan jama'a
[gyara sashe | gyara masomin]Year | Pop. | ±% |
---|---|---|
1793 | 1,754 | — |
1800 | 1,635 | −6.8% |
1806 | 1,708 | +4.5% |
1821 | 1,705 | −0.2% |
1831 | 1,806 | +5.9% |
1836 | 1,522 | −15.7% |
1841 | 1,530 | +0.5% |
1846 | 1,547 | +1.1% |
1851 | 1,553 | +0.4% |
1856 | 1,574 | +1.4% |
1861 | 1,648 | +4.7% |
1866 | 1,635 | −0.8% |
1872 | 1,720 | +5.2% |
1876 | 1,638 | −4.8% |
1881 | 1,713 | +4.6% |
1886 | 1,936 | +13.0% |
1891 | 2,063 | +6.6% |
1896 | 2,255 | +9.3% |
1901 | 2,402 | +6.5% |
1906 | 2,544 | +5.9% |
1911 | 2,681 | +5.4% |
1921 | 2,961 | +10.4% |
1926 | 3,132 | +5.8% |
1931 | 3,240 | +3.4% |
1936 | 3,163 | −2.4% |
1946 | 3,345 | +5.8% |
1954 | 3,172 | −5.2% |
1962 | 3,772 | +18.9% |
1968 | 5,124 | +35.8% |
1975 | 5,808 | +13.3% |
1982 | 5,722 | −1.5% |
1990 | 6,129 | +7.1% |
1999 | 6,820 | +11.3% |
2007 | 6,917 | +1.4% |
2012 | 6,846 | −1.0% |
2017 | 6,908 | +0.9% |
Gwamnati
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 1 ga Agustan 1948, an cire kashi 17% na yankin Auvers-sur-Oise kuma ya zama gundumar Butry-sur-Oise .
Magajin garin na yanzu itace Isabelle Mézières. An fara zaben ta a shekarar 2014, sannan aka sake zabe ta a watan Maris shekara ta 2020.
Al'adu
[gyara sashe | gyara masomin]Wuraren tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Gina cocin ya samo asali ne tun daga ƙarni na 11. Louis VI le Gros (1081-1137) ya mallaki manor a Auvers, inda yakan zo farauta. A shekara ta 1131 dansa Philippe, wanda shi ne yarima mai jiran gado, ya fado daga kan dokinsa ta hanyar kuma ya mutu. An gina ɗakin bauta a wurin da aka binne shi kuma wannan daga baya ya zama cocin Notre-Dame de l'Assomption: a cikin shekarar 1915 wurin ya shiga cikin abubuwan tarihi na duniya. Tare da gidan sarautar, suna wakiltar manyan yankunan tarihi na al'adun birni, inda shahararrun masu zane-zane suka zo a cikin karni na 19, kamar Daubigny, Bourges, Bernard, Pearce, Bastard, Boggio ko Wickenden.
-
Church Notre-Dame de l'Assomption
-
Croix du Montcel
-
Hoton Charles-François Daubigny
Gidajen tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]- The musée Daubigny, wanda yake a cikin mazaunin Colombières, an ƙirƙira shi ne a cikin shekarar 1986 wanda Ofishin Yawon Bude idanu suka yi hakan. Gidan kayan tarihin ya kunshi kusan ayyuka dari na Daubigny, kamar zane-zane, fenti da sassake-sassaken sa.
- Musée de l'absinthe (Absinthe Museum), wanda ke unguwar rue Callé, ya kunshin kayan tarihi na abubuwan sha.
Van Gogh
[gyara sashe | gyara masomin]Dr. Paul Gachet ya yi rayuwa a Auvers-sur-Oise. Ya saba da masu zanen avant-garde na lokacin. Ta hanyar wannan alaka, Vincent van Gogh ya koma Auvers don yayi masa magani, kodayake ya iske likitan a cikin wani yanayi mafi muni fiye da yadda yake. Gachet ya yi abota da Van Gogh kuma ya zana hotonsa har sau biyu, daya daga cikinsu, Hoton Dr. Gachet, an sayar da shi a wajen wani gwanjon akan kudi sama da $80m (£48m) a shekara ya 1990.[2]
Van Gogh ya mutu ne sakamakon harbin kansa da yayi a kirji. An adanaa dakin da ya mutu saboda tarihi. Jami'ar Van Gogh ta mallaki Auberge Ravoux, kuma ita ke shirya ziyarar ɗakin Van Gogh kuma ta buɗe gidan cin abinci a dakin.[3] Auvers-sur-Oise shine wurin hutawa na ƙarshe na duka Vincent da ɗan'uwansa Theo van Gogh, wanda ya mutu bayan watanni shida.
-
L'Auberge Ravoux, inda Vincent van Gogh ya shafe watanni na ƙarshe kuma inda ya mutu. Yanzu gidan abinci ne.
-
Duba daga matakalar da ke kaiwa zuwa ɗakin Van Gogh a cikin L'Auberge Ravoux
-
Kaburburan Vincent da Theo van Gogh a Auvers-sur-Oise.
-
Hoton Dr. Gachet na Vincent van Gogh
-
Filin Alkama tare da Crows, ɗayan zane-zane na ƙarshe na Van Gogh
-
Lambun Daubigny, mai yiwuwa zanen ƙarshe na Van Gogh
-
Camille Pissarro , Makiyayi a Valhermeil, Auvers-sur-Oise, Gidan Tarihi na Gidan Tarihi
-
Samfuri:Interlanguage link multi, Auvers-sur-Oise (Bâteau lavoir à Auvers), ca.1870
-
Frédéric Samuel Cordey, Ruelle à Auvers sur Oise, kusan 1903
-
Paul Cézanne, Duban Auvers-sur-Oise, 1873-75
Sufuri
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai tashoshin jiragen kasa guda biyu a garin Auvers-sur-Oise na Transilien Paris – Nord : Chaponval da Auvers-sur-Oise . Tashoshin duka suna bi ya layin Pontoise - Creil . Tsakanin Afrilu da Oktoba, a ranakun Asabar, Lahadi da ranakun hutu, jiragen kasa kai tsaye suna tafiya daga Paris Gare du Nord zuwa Auvers.
Hakanan kuma akwai tashoshin bas guda biyu aAuvers : 95 07 da 95 17.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Ƙungiyoyin sashen Val-d'Oise
- Auvers a lokacin Vincent van Gogh
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Articles with French-language sources (fr)
- Wikipedia articles with BNF identifiers
- Wikipedia articles with GND identifiers
- Wikipedia articles with LCCN identifiers
- Wikipedia articles with MusicBrainz area identifiers
- Pages with red-linked authority control categories
- Wikipedia articles with NKC identifiers
- Wikipedia articles with SUDOC identifiers
- Wikipedia articles with VIAF identifiers
- Wikipedia articles with WorldCat-VIAF identifiers
- Pages using the Kartographer extension